Mutane biyu wato Ahmed Ali mai shekaru 28, da kuma Suhah Mussa mai shekaru 27, dukkansu 'yan kasar Libya ne. An ce da karfe 12 na ranar 25 ga watan nan da muke ciki, 'yan sanda suka iza keyar wadannan mutane kotun ta Malta domin gurfanar da su gaban shari'a.
Ana zargin mutanen biyu da aikata laifuffukan ta'addanci, da satar jirgin sama, da yiwa fasinjojin da suke cikin jirgin saman barazana, da kuma rike makamai na bogi. Ana dai hasashen cewa idan har aka tabbatar da laifukan da ake tuhumar su da aikatawa, za su iya fuskantar daurin rai da rai.
Sai dai mutane biyu su musanta aikata laifukan da ake zargin su a yayin zaman kotun, kuma ya zuwa yanzu, ba su mika bukatar beli ba. (Maryam)