An ce, wannan jirgin sama samfurin A320 mallakar kamfanin Afriqiyah Airways ne na kasar Libya. A lokacin faruwar lamarin, jirgin saman na zirga-zirga cikin kasar, kafin masu garkuwar su biyu su bukaci a canja hanyar da yake bi ko kuma su tayar bom a cikin sa. (Bilkisu)