Gidan talabijin din kasar Malta ya bayar da labarin cewa, an sako dukkan mutane 116 dake jirgin saman fasinja na kasar Libya da aka yi garkuwa da shi a ranar 23 ga wata, masu yin garkuwar su biyu kuma sun mika kansu.
Wannan jirgin saman fasinja na kasar Libya ya sauka a filin jiragen saman kasa da kasa na Malta bayan da aka yi garkuwa da shi a ranar 23 ga wata, fasinja dake jirjin saman sun hada da maza 82, mata 28 da wani jariri, baya ga wasu ma'aikatan jirgin 7. Masu yin garkuwar biyu sun ce, suna daukar gurneti, suna iya fashe jirgin a duk lokacin da suke so.
Kafofin watsa labaru na Malta sun bayar da labari cewa, masu yin garkuwa sun bukaci a kafa wata sabuwar jam'iyyar dake goyon bayan tsohon shugaban kasar Libya Moammar Gaddafi, idan an biya bukatunsu, to za su sake dukkan fasinjan dake jirgin saman. Rahotannin sun ambato shugaban birnin Sebha na Libya na cewa, alamu a farko sun nuna cewa, masu yin garkuwa suna da nufin neman samun mafakar siyasa ne a Malta. (Bilkisu)