Cutajar ya bayyana cewa, ana ci gaba da yin bincike kan lamarin sace jirgin saman, don haka ba a tabbatar da lokacin gurfana da su a gaban kotu ba. Ya ce, babu shaida dake tabbatar da cewa, ko su biyun suna da nasaba da kungiyar yan ta'adda.
Haka zalika, Cutajar ya bayyana cewa, wadannan mutane biyu ba su gabatar da bukatunsu ba.
Wani jirgin saman kasar Libya dake dauke da mutane 118 ya sauka a filin jiragen saman kasa da kasa na kasar Malta, bayan da aka sace shi a ranar 23 ga wata, ba da jimawa ba aka saki mutane 116 da aka yi garkuwa da su. Bisa labarin da gidan telebijin na kasar Malta ya bayar, an ce, mutanen biyu su ne Mousa Shada da Ahmed Ali, suna dauke bindigar hannu yayin da suka sace jirgin saman.
Yanzu ana tsare da mutanen biyu inda za su fuskanci shara'a. Dukkan fasinjojin dake cikin jirgin saman sun koma kasar Libya da safiyar ranar 24 ga wata. (Zainab)