in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon ya kalubalanci bangarorin Libya da su daidaita rikici tare
2016-12-18 13:10:57 cri
A jiya Asabar, babban magatakardan MDD Ban Ki-moon ya bada sanarwa kan cika shekara guda bayan daddale yarjejeniyar siyasa a Libya, inda ya yi kira ga bangarori daban daban na kasar da su amince su shiga tattaunawar sulhu da juna ta hanyar siyasa, domin daidaita rikicin da ake fuskanta a kasar.

Ban Ki-moon ya jinjinawa jama'ar kasar Libya bisa juriya na shiga yunkurin daidaita rikicin siyasar kasar a shekara guda da ta wuce, ya yi nuni da cewa, an kafa kwamitin firaministan kasar a shekarar 2016, yayin da aka kara fitar da man fetur, yayin da kuma aka samu gagarumin cigaba wajen yaki da ta'addanci a duk fadin kasar.

A sa'i daya, Mr. Ban ya bayyana cewa, ana cigaba da fuskantar tafiyar hawainiya wajen tabbatar da yarjejeniyar siyasa ta Libya, wadda ba ta tabbatar da zaman lafiya da tsaro da jama'ar kasar ke bukata ba. Shi ya sa ya kalubalanci bangarorin da ba su shiga yunkurin siyasa ba da su kokarta daidaita rikicin kasar tare da juna, kuma ya ce, MDD za ta ci gaba da nuna goyon baya ga jama'ar kasar Libya.

A shekarar 2011, bayan rushewar mulkin Gaddafi, aka shiga yanayin tangal tangal a kasar Libya. Kungiyoyin ta'addanci da kungiyoyi masu tsattsauran ra'ayi sun kara karfinsu a daidai wannan lokaci a kasar. Bisa shiga tsakani na MDD, a ranar 17 ga watan Disamban shekarar 2015, bangarorin biyu da suke gaba da juna a Libya suka daddale yarjejeniyar siyasa ta kasar, inda suka amince da kafa gwamnatin hadin kan al'ummar kasar ta Libya.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China