Mr Sarraj ya sanar da 'yantar da birnin Sirte a hukunce ne a jawabin da ya gabatar ta gidan talabijin a wannan rana, kana an kawo karshen matakan sojan da aka dauka na watanni 8. A hannu guda kuma, ya bayyana cewa, ba a kawo karshen yakin da za a yi da kungiyar IS ba.
Tun a watan Mayun wannan shekarar ce, gwamnatin hadin kan al'umma ta kasar Libya ta kafa wata rundunar tsaro domin yaki da mayakan kungiyar IS dake mamaye da birnin Sirte, inda ta yi nasarar kwace galibin yankunan wannan birnin cikin gajeren lokaci. Dakarun kungiyar IS dai sun dade suna rike da wasu yankuna, inda bangarorin biyu suka yi rika kaiwa juna hare-hare.
A ranar 5 ga watan nan da muke ciki ne, gwamnatin hadakar kasar ta sanar da cewa, rundunar tsaron gwamnatin ta riga ta fatattaki dakarun kungiyar IS da ke birnin Sirte, lamarin da ke nuna cewa, yanzu gwamnati ce ke da iko da birnin gaba daya. (Maryam)