A cewar kakakin ofishin na Majalisar Dinkin Duniya, asusun na da nufin samar da wani yanayi na kyautata tsarin siyasa, ta yadda zai kawo karshen rikice-rikice a kasar.
Duk da yarjejeniyar da majalisar Dinkin Duniya ta samar tsakanin jami'yyun adawa na kasar Libya a watan Disamban bara, har yanzu, kasar na ci gaba da fuskantar rarrabuwar kawuna tsakanin gwamnatoci biyu da majalisun dokoki.
Har ila yau, a Ranar Talatar ne, kwamitin sulhu na majalisar Dinkin Duniya ya amince da fadada aikin taimako na majalisar a Libya zuwa watanni tara, wato nan da wata Satumban shekarar 2017.(Faeza Mustapha)