in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na maraba da matsayar bai daya da kasashen Rasha, Iran da Turkiya suka cimma kan batun Syria
2016-12-21 20:48:33 cri
Rahotanni na cewa kasashen Rasha, da Iran da kuma Turkiya sun cimma ra'ayi na bai daya, game da kudurin fadada sassan da za a tsagaita bude wuta a kasar Syria, da samar da hanyar gudanar da ayyukan ceto na jin kai, da kuma kwashe fararen hula.

Kaza lika kasashen uku sun bayyana cewa, a shirye suke su taimakawa gwamnatin Syria wajen daddale yarjejeniya da 'yan adawa, za kuma su kasance masu tsayawa wajen kare yarjejeniyar.

Game da wannan batu, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta bayyana a yau Laraba cewa, Sin na maraba da kokarin da ake yi game da warware batun Syria a siyasance, da kuma tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a kasar. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China