Da yake tsokaci game da hakan, mamban kwamitin lura da zamantakewar al'umma na ma'aikatar tsaron kasar Rasha, kana shahararren mai sharhi kan harkokin aikin soja, Igor Korotchenko ya bayyana cewa, mai yiwuwa ne dakarun 'yan adawar Syria za su dauki wasu matakai a yayin da suke janyewa daga yankin. Duk da haka, gwamnatin Rasha na fatan daukacin dakaru masu adawa da gwamnati dake garin Aleppo, ciki har da 'yan kungiyar masu tsattsauran ra'ayi za su janye, domin samar da yanayi mai kyau na aikin jin kai.
Kaza lika babban hafsan hafsoshin rundunar sojan Rasha, Valery Gerasimov ya bayyana cewa, sojojin Syria sun riga sun mamaye kashi 98 bisa dari na yankunan dake birnin Aleppo. Ya ce kawo yanzu, Rasha da Syria suna share fagen warware rikici tsakanin bangarori daban daban na Syria ta hanyar siyasa.
Har ila yau jami'in ya yi kira ga kasashen duniya da su kara kokarin hadin gwiwa, domin yaki da ta'addanci bisa jagorancin MDD. (Fatima)