in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan harkokin wajen Rasha da sakataren harkokin wajen Amurka sun zanta ta waya game da halin da ake ciki a kasar Syria
2016-12-15 13:32:10 cri
Sakataren harkokin wajen kasar Amurka John Kerry ya zanta ta wayar tarho da ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergei Lavrov a jiya Laraba game da halin da ake ciki a birnin Aleppo na kasar Syria.

Yayin zantawar tasu, Mr. Lavrov ya bayyana cewa, dakaru masu adawa da gwamnatin Syria sun ki amincewa su tsagaita bude wuta, don haka Rasha ta kalubalanci Amurka yi matsin lamba ga dakarun da take goyon baya.

A nasa bangare, Kerry ya zargi sojojin gwamnatin Syria da gurgunta yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Aleppo, kana ya jaddada bukatar dakatar da zubar jini ta hanyar tsagaita bude wuta. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China