Zuma, ya furta hakan ne a loakcin da yake jawabi game da hare haren ta'addanci da aka kaddamar a kasashen Yemen, Turkey da Somalia a karshen makon da ya wuce.
Shugaban ya ce a madadin gwamnati da al'ummar kasar Afrika ta kudu, suna yiwa kasashen na Yemen, Turkey da Somalia ta'aziyyar hasarar rayuka jama'a wadanda hare haren suka haddasa.
Zuma ya ce, gwamnatin Afrika ta kudun ta yi Allah wadai da munanan hare haren ta'addanci da aka kaddamar a kasashen uku, wanda ya haddasa hasarar rayukan jama'a.
Ya ce sam sam ba za'a aminci duk wani nau'i na ayyukan ta'addanci ba.
Shugaban na Afrika ta kudu ya ce, hare haren ta'addancin da ake kaddamarwa kan fararen hula sun sabawa dokokin kasa da kasa da kuma dokokin kare hakkin dan Adam.
An karshen makon da ya wuce ne dai aka kaddamar da hare haren ta'addanci a biranen Aden, Istanbul da kuma Mogadishu, wadanda suka haifar da hasarar rayuka da kuma jikkata mutane da dama. (Ahmad)