A jiya Litinin ne, Wu Haitao, mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD ya yi kira ga kasashen duniya da su inganta hadin gwiwarsu ta fuskar dokokin yaki da ta'addanci, a kokarin bullo da wani tsarin shari'a na bai daya a duk fadin duniya ta yadda za a samu nasarar yaki da 'yan ta'adda.
A wannan rana, kwamitin sulhu na MDD ya shirya wani taro dangane da inganta hadin gwiwa a tsakanin kasa da kasa kan yadda za a aiwatar da shari'a, tare da zartas da kuduri. A cikin jawabinsa, Wu Haitao ya ce, bullo da doka kan yaki da ta'addanci zai aza harsashi ta fuskar shari'a a fannonin yaki da 'yan ta'adda da kuma hada kai wajen yaki da su. Ya ce, ya kamata kasashen duniya su taimakawa kwamitin sulhu, da mara wa juna baya wajen tsara da kuma sabunta dokokin yaki da ta'addanci bisa la'akari da sabbin barazanar da ake fuskanta yanzu. Sa'an nan kuma, kamata ya yi a mutunta 'yancin kasashe a fannonin kafa doka da kuma aiwatar da doka, bisa hakikanin halin da suke ciki. (Tasallah Yuan)