Ahmed Abu Zeid, shi ne mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Masar ya ce, ma'aikatar tana bada muhimmancin gaske wajen goyon bayan duk wani mataki da zai kawo fahimtar juna tsakanin bangarorin kasar ta Libya, da kuma aiwatar da yarjejeniyar Skhirat da tabbatar da amfani da kundin tsarin mulkin kasar.
Majburi, ya yaba da irin kokarin da gwamnatin Masar ke yi na ganin an samu dawwamamman zaman lafiya a kasar Libya, da kuma irin namijin kokarin da take yi na yin aiki tare da mahukuntan kasar Libyan domin amfanin a'lummar kasar.
A karshen watan Yuli ne, kasar Masar ta jagoranci wani muhimmin taron tattaunawa tsakanin shugaban tsagin gwamnatin Libya dake samun goyon bayan MDD Fayez Serraj, da na shugaban majalisar dokokin Libya Aqila Saleh, a wani yunkurin dinke barakar dake tsakanin manyan shugabannin siyasar kasar.
Sai dai ana ganin cewar, yunkurin da kasar ta Masar ke yi na tabbatar da zaman lafiya a kasar Libya, ba zai rasa nasaba da tabbatar da tsaron kanta ba, sakamakon makwabtakar dake tsakanin kasashen biyu. (Ahmad)