Tun daga watan Mayu zuwa yanzu, gwamnatin Libya ta kafa rundunar soja mai tsaron gwamnati domin kai samame kan birnin Sirte dake hannun kungiyar IS, tare da mamaye mafi yawansa a cikin gajeren lokaci. Amma a kan wasu tituna, rarar dakarun kungiyar IS su kan mai da martani tare da gwanayen harbe da kai harin kunar bakin wake da motocin da aka dasa boma-bomai. A sabili da haka, an shiga halin kiki-kaka.
A shekarar 2011, bayan kifar da mulkin Muammar Gaddafi, kasar ta fada cikin yakin basasa. Kungiyoyi masu tsattsauran ra'ayi da na ta'addanci sun kara karfinsu a kasar a daidai wannan lokaci. A cikin wannan yanayi kuma, kungiyar IS ta mamaye biranen Sirte, Derna da sauransu, tare da kafa sansanoni a kusa da biranen Tripoli, Benghazi da dai sauransu. (Fatima)