in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhu na MDD ya bukaci bangarorin daban daban na Libya da su gaggauta aiwatar da yarjejeniyar siyasa
2016-12-08 15:25:03 cri
A jiya Laraba 7 ga wata ne, kwamitin sulhu na MDD ya fidda wata sanarwa, inda ya nuna damuwarsa kan yanayin siyasa da tsaro a kasar Libya, inda ya yi kira ga bangarori daban daban na kasar Libya da su gaggauta aiwatar da yarjejeniyar siyasa da aka cimma.

Haka kuma, cikin sanarwar, kwamitin ya bayyana cewa, a halin yanzu, ana fuskantar mummunan sabani a tsakanin bangarorin siyasar kasar, lamarin da ya gurgunta yanayin tsaro, tattalin arziki da harkokin jin kai a kasar. Kaza lika, ci gaba na rikice-rikice a tsakanin kungiyoyin dakaru a babban birnin kasar, Tripoli ya janyo hankalin kwamitin sulhu na MDD kwarai da gaske, inda ya kuma bukaci bangarori daban daban da abin ya shafa da su tsagaita bude wuta ba tare da bata lokaci ba.

Bugu da kari, an jaddada bukatar bangarori daban daban na kasar Libya su shiga a dama da su a kokarin ganin an aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma tare da taimakawa bangarori daban daban da abin ya shafa su hada kai da kwamitin firaminista na kasar, domin hanzarta warware muhimman matsalolin da kuma hada kai wajen farfado da kasar baki daya. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China