in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Algeriya zata kai kayan tallafi Libya
2016-11-03 10:46:43 cri
Gwamnatin Algeriya tace zata aike da kayan agajin ga al'ummar kasar Libya dake zaune a kan iyakokin kasashen biyu.

Ma'aikatar harkokin wajen kasar ta bayyana cewar nan bada jimawa ba za'a kai kayan agajin ga mutanen dake cikin halin bukata, bisa la'akari da dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, sai dai ba'a bayyana takamamman kayayyakin ko adadin da za'a kai ba.

Da ma dai mahukunta kasar ta Algeriya sun bada wuraren zama ga daruruwan alummar kasar Libya wadanda yakin basasa na shekarar 2011 ya raba su da matsugunnansu, Algeriya ta bukaci bangarorin da basa ga maciji da juna a kasar ta Libya dasu yi kokari wajen tabbatar da kafa gwamnatin hadin kan kasa domin magance kalubalen tsaro dake addabar kasar.

Bugu da kari, Algeriya ta tura dakarunta sama da 50,000 zuwa kan iyakar kasar mai tazarar kilomita 1000 da kasar Libya, domin shirin ko-ta-kwana game da yiwuwar fuskantar hare haren mayaka masu kaifin kishin Islama dake da alaka da al-Qaida.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China