Sin tana son yin hadin gwiwa tare da Amurka a fannin gina ayyukan more rayuwa
Zababben shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bayyana a cikin jawabinsa na lashe zaben shugabancin kasar Amurka a kwanakin baya cewa, zai bullo da shirin gina kayayyakin more rayuwa don sake farfado da kayayyakin more rayuwa da suka lalace a kasar. Game da wannan batu, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang ya bayyana a yau Litinin cewa, Sin tana begen fadada hadin gwiwa tare da sabuwar gwamnatin kasar Amurka a fannoni daban daban. (Zainab)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku