in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi ya zanta da zababben shugaban Amurka Donald Trump ta wayar tarho
2016-11-14 15:38:46 cri
A Litinin din nan ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya zanta ta wayar tarho da shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump, inda ya taya Mr. Trump din murnar lashe zaben da ya gabata a 'yan kwanaki.

Shugaba Xi ya ce cikin shekaru 37 da suka gabata, Sin da Amurka sun kulla huldar diflomasiyya mai nagarta, irin dangantakar da ke ci gaba da bunkasa yadda ya kamata.

Kaza lika shugaban na Sin ya jaddada cewa hadin gwiwar sassan biyu ne kadai zai ci gaba da baiwa kasashen damar kara inganta alakar su bisa hanya mafi dacewa.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China