An samu labarin daga kakakin watsa labaru na gwamnatin hadin kan al'ummar kasar cewa, bayan kazamin yaki na kwanaki uku a tsakanin sojojin tsaron gwamnatin da dakaru masu tsattsauran ra'ayi, an cimma nasarar kwato yawancin birnin dake hannun kungiyar IS, kuma aka ceto wadannan mutane 13, ciki har da 'yan kasar Eritoria 11, 'dan kasar Turkiya 1 da kuma 'dan kasar Masar 1.
A shekarun nan, kungiyoyin ta'addanci da na masu tsattsauran ra'ayi suna amfani da yanayin tashe-tashen hankula a kasar Libya don habaka karfinsu a kasar. Tun daga watan Mayu na bana, gwamnatin hadin kan al'ummar Libya ta kafa kawancen sojojin sa kai dake yaki da kungiyar IS, don kara murkushe dakarun IS dake Sirte da sauran yankuna, kuma a watan Agusta ne ta sanar da cewa, an samu babban ci gaba kan matakan soja da suka dauka. (Bilkisu)