Jiya Jumma'a, aka yi babban taron kasa da kasa da ya shafi harkokin mata da batun talauci mai tsanani a birnin Rome na kasar Italiya, inda halartar taron suka yi kira da a mai da hankali kan inganta harkokin zaman daidai wa daida a tsakanin maza da mata da kuma baiwa mata iko yadda ya kamata, ta yadda za a ba da taimako wajen kawar da talauci mai tsanani da kuma karancin abinci.
Babban sakataren hukumar abinci da ayyukan gona ta MDD Jose Graziano da Silva, ya bayyana a yayin taron cewa, mata suna ba da muhimmiyar gudummawa cikin ayyukan gona, musamman matan dake zaune a yankunan karkara, wadanda suke bada taimako matuka wajen tabbatar da cimma burin samun dauwamammen ci gaba.(Maryam)