Xi Jinping ya ce, a halin yanzu, ya kamata matasan kasa da kasa su bude idanunsu don ganin harkokin kasa da kasa, da karfafa aniyarsu wajen yin hadin gwiwa da takwarorinsu na kasa da kasa ta hanyar neman ilmi, ta yadda za su iya gina wata makoma mai kyau ga dukkan bil Adama a fadin duniya.
Kaza lika, shugaba Xi ya jaddada cewa, musayar harkokin ba da ilmi dake tsakanin kasar Sin da Amurka, ya ba da babbar gudummawa wajen ciyar da fahimtar juna, da zumunci da kuma dangantaka a tsakanin Sin da Amurka gaba, shi ya sa ya kamata kasashen Sin da Amurka su ci gaba da habaka da kuma inganta hadin gwiwar dake tsakaninsu a wannan fanni, ta yadda zai kasance mai fitowa sosai cikin harkokin musayar al'adu a tsakanin Sin da Amurka.
Bugu da kari, ya ce, ana fatan kwalejin Schwarzman za ta kasance wata kyakkyawan dandali na kasa da kasa wajen horas da masana don samun kwarewa a fannonin da abin ya shafa, da samarwa matasan kasa da kasa dammar yin karatu a kwalejin, ta yadda za su iya karfafa musaya da fahimtar juna a tsakaninsu, yayin da kuma zasu bude idanunsu ta hanyar yin shawarwari da kuma koyar da juna, sa'an nan za su iya yin hadin gwiwa da bada gudummawa yadda ya kamata wajen tallafawa al'ummomin kasa da kasa. (Maryam)