A sabo da haka, MDD ta fara wani biki na kwanaki 16 da aka yi wa taken "A yi wa duniya adon launin orange, a tara kudade domin yin amfani da su wajen yaki da cin zarafin mata da yara mata", kuma an shirya bikin ne domin kara sanin mutanen kasa da kasa kan harkokin tashe-tashen hankulan da aka yi wa mata, ta yadda za a iya karbar kudade daga wajensu don ba da taimako kan wannan shiri yadda ya kamata.
Haka kuma, bisa kididdigar da MDD ta yi, an ce, kashi daya bisa uku na matan duniya sun taba gamuwa da tashe-tashen hankula da aka aikata musu, kana, galibin mutanen da suka aikata musu irin wannan laifufuka su ne iyalansu.
A halin yanzu, mutanen duniya sun lura da cewa, tashe-tashen hankulan da aka yi wa mata da yara mata, ya kasance mugun laifin keta hakkin dan Adam, lamarin dake kawo barazana wajen kiyaye lafiyar al'ummomin kasa da kasa, yayin da yake haddasa illa ga dauwamammen ci gaban duniya.
Sabo da haka, babban magatakardan MDD Ban Ki-moon ya gabatar da wani jawabi a yayin ranar kawar da tashe-tashen hankula a gida, inda ya bukaci a karfafa yin rigakafi kan irin wannan matsalar, da daukar matakai yadda ya kamata a lokacin da aka aikata laifin muzgunawa mata, kuma akwai abubuwa da dama da za a yi wajen kawar da irin wannan laifi a duniya. (Maryam)