Masana daga kasashen Afrika, har ma da sauran kasashen duniya ne suka yi wannan tsokaci a jiya Talata, a lokacin gabatar da jawabai a gaban dalibai sama da 40 wadanda suka fito daga kasashen Afrika 14, dake halartar taron jami'o'i na kasashen renon Ingila wato commonwealth a Kigali babban birnin kasar Rwanda.
Taron na tsawon mako guda ne, an fara gudanar da shi a ranar Lahadi, zai bada dama ga daliban kasashen don tattauna muhimman batutuwa da suka shafi kalubalen dake hana cigaban kasashen duniya, tare da nazartar hanyoyin magance matsalolin.
A cewar farfesa Mommo Muchie, na jami'ar kimiyya da fasaha ta Afrika ta kudu, ya kamata matasan Afrika su shiga aikin gona, sai dai yace lamarin yana bukatar agaji daga shugabanni, kuma akwai bukatar shugabannin su samar da kudade masu yawa don zuba jari a fannin aikin gona.