Babban magatakardan MDD Ban Ki-moon ya yi kira ga kasashen duniya da su rika sanya mata a shirye-shiryen hana aukuwar tashe-tashen hankula, da tabbatar da zaman lafiya a duniya.
Mr Ban ya ce, mata da 'yan mata suna da gagarumar rawar da za su taka a dukkan shirye-shiryen tabbatar da zaman lafiya da ake zayyanawa a duniya.
Ban Ki-moon ya bayyana hakan ne a jawabin da ya gabatar yayin muhawarar da kwamitin tsaron majalisar ya shirya game da mata, tsaro da zaman lafiya. Ya ce, duk da irin ci gaban da aka samu, har yanzu akwai jan aiki, ganin yadda ake ci gaba da gallazawa mata da 'yan mata, ciki har da ma'aikatan wanzar da zaman lafiya na MDD, da kuma yadda ake mayar da mata saniyar ware a harkokin siyasa, da shirin samar da zaman lafiya na kasar Syria ko kuma Yemen.
A saboda haka, ya bukaci kasashe mambobin kwamitin tsaron majalisar guda 15, da su rika sanya mata da 'yan mata a kan gaba cikin ayyukan samar da zaman lafiya na majalisar. Kana su rika sauraran kungiyoyin fafaren hula, musamman kungiyoyin mata yayin da ake tattauna hanyoyin magance rigingimu da samar da zaman lafiya a sassan daban-daban na duniya.(Ibrahim)