A cewar babban jami'in bankin mai kula da harkokin fasahar sadarwa Salieu Jack, shirin zai gudana ne ta hanyar amfani da na'urar salula, zai kuma baiwa mata damar samun rancen kudin inganta sana'o'in su, da samun horo, da musayar kwarewa, da ingantattun bayanai, ana kuma fatan bayan kankamar shirin, matan dake zaune a yankunan kudu da hamadar sahara za su samu karin guraben ayyukan yi, daga kaso 4 bisa dari zuwa kaso 10 bisa dari nan da shekarar 2022.
Bisa tsarin aiwatar da shi, bankin na raya Afirka ya alkawarta game sassan kungiyoyin nahiyar Afirka kamar su COMESA, da EAC da ECOWAS cikin shirin. Kasashen Afirka 36 ne dai ake sa ran za su ci gajiyar wannan tallafi, za kuma a aiwatar da shirin cikin shekaru 3, tun daga shekarar 2017 mai zuwa.
Ana hasashen cewa, da zarar an kaddamar da shirin, masu cin gajiyar sa a ko wane wata, za su kai mata 50,000 nan da shekarar 2022. Kaza lika karuwar guraben ayyukan yi tsakankanin matan nahiyar zai haifar da karin kaso 10 bisa dari, na jimillar guraben ayyukan yi a nahiyar baki daya.(Saminu Alhassan)