A yayin taron karawa juna sani na mata kan harkokin tattalin arzikin teku a lokacin taron koli na musamman kan harkokin tsaron teku na kungiyar tarayyar kasashen Afirka da aka yi a jiya Jumma'a, Madam Zuma ta bayyana cewa, ana fatan shigar da mata cikin aikin neman bunkasuwar tattalin arziki na teku, saboda lamari ne da zai baiwa mata 'yanci da kuma dogaro da kansu, inda za su sami ayyukan yi, da kafa kamfanoni na kashin kansu, ta yadda za su bada gudummawa wajen raya tattalin arzikin nahiyar Afirka. (Maryam)