Alkaluman da kungiyar ta fitar sun nuna cewa, kasar Sin ta kiyaye wani yanayin da take ciki game da samun karuwar neman lambar mallakar kira, da lambar kira, ko da yake yanzu a duk duniya ba a samun karuwa sosai a wannan fanni.
A nasa bangare, Chen Hongbing, daraktan ofishin kungiyar ikon mallakar ilimi ta duniya reshen kasar Sin, ya bayyanawa 'yan jaridu cewa, kungiyar ta yaba wa kasar Sin, game da yadda harkar ikon mallakar ilimi take samun ci gaba cikin sauri a kasar. Haka zalika kungiyar tana sa ran ganin manufofin kasar Sin, da suka hada da shirin "ziri daya da hanya daya", wato zirin raya tattalin arziki na hanyar siliki, da hanyar siliki dake kan teku ta karni na 21, gami da sauran matakan kasar, za su taimakawa kokarin yada fasahohi, da kayayyaki, da hidima na kasar Sin zuwa sauran kasashe.
A cewar Chen Hongbing, domin raya tattalin arzikin Sin, ana bukatar kirkiro sabbin fasahohi, yayin da kare ikon mallakar ilimi zai kasance mataki mafi dacewa wajen kara azama ga kokarin kirkiro sabbin fasahohi. Don haka a ganinsa, kasar Sin za ta mai da muhimmanci matuka ga ikon mallakar ilimi, a yunkurinta na neman samun ci gaban tattalin arziki. (Bello Wang)