Kamfanin dillancin labarun kasar Masar (MENA) ya labarta a yau Talata 13 ga wata cewa, ma'aikatar harkokin cikin gida ta kasar ta bayyana a cikin wata sanarwar da ya bayar cewa, jagoran kungiyar 'yan uwa Musulmi na da hannu a fashewar bom da ta auku a wani coci dake birnin Alkahira. Inda ake tuhumarsa da laifin ba da horo da kudi ga wadanda suka kai harin.
A ranar 11 ga wata bayan aukuwar harin, kungiyar 'yan uwa Musulmi ta Masar ta sanar da cewa, ba ta da hannu a wannan harin. (Tasallah Yuan)