in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An gurfanar da mutane 292 da aka zarge su da aikata laifin ta'addanci a gaban kotun soja ta kasar Masar
2016-11-21 10:25:16 cri
Bisa labarin da kamfanin dillancin labaru na MENA ya bayar, hukumar bincike kan manyan laifuffuka ta kasar Masar ta gurfanar da mutane 292, da aka zarge su da aikata laifin kai hare-haren ta'addanci a zirin Sinai da yunkurin kisa shugaban kasar Abdel-Fattah al-Sisi, a gaban kotun soja ta kasar.

Labarin ya bayyana cewa, wadannan mutane 292 sun fito daga kungiyar masu tsattsauran ra'ayi ta "Sinai Province of the Islamic State",wato 'jihar Sinai karkashin mallakar kungiyar IS', dake arewacin jihar Sinai ta kasar Masar.

Tsohon sunan kungiyar "Jihar Sinai" shi ne Ansar Bait al-Maqdis, an kafa ita bayan da aka samu juyin mulki a kasar Masar a shekarar 2011, kungiyar na gudanar da ayyukanta a zirin Sinai, da kai hare-hare ga 'yan sanda sau da dama, dalilin haka ne ya sa kasar Masar da ta Amurka da sauran kasashe suka sanya ta cikin jerin kungiyoyin ta'addanci. Tun daga shekarar 2014, kungiyar ta sanar da biyayyarta ga IS, tare da canja sunanta zuwa kungiyar "Jihar Sinai karkashin mallakar kungiyar IS". (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China