Shugaba al-Sisi ya bayyana cewa, matashin da ya kai harin ta'addancin dan kunar bakin wake ne mai suna Mahmoud Shafiq, kana an riga an kama saura mutane hudu da aka zarga da hannu cikin kitsa harin, kuma tuni hukumar kiyaye tsaro ta kasar ta fara neman wasu sauran mutane biyu dake da alaka da harin.
Da safiyar ranar Lahadi ne dai wani bam ya tashi a wata coci dake birnin Alkahira. Kana hukumar kiwon lafiya ta kasar ta bayyana cewa, ya zuwa yanzu mutane 24 ne suka rasa rayukan su sakamakon fashewar, yayin da wasu mutanen 49 suka jikkata. (Zainab)