Cikin wata sanarwa da kakakin sa ya fitar a jiya Lahadi, Ban Ki Moon ya yi fatan za a kai ga hukunta wadanda suka aikata wannan mummunan laifi.
Shi ma dai kwamitin tsaron MDDr ya yi kakkausan suka game da aukuwar wannan hari, yana mai cewa ya zama wajibi a hukunta wadanda suka aikata shi.
Rahotanni na cewa wasu ne da ba a tantance da su ba, suka dasa Bam din mai nauyin kilogiram 12 a majami'ar dake makare da masu ibada, wadda ke unguwar Abassiya, wanda kuma fashewarsa ta hallaka tare da jikkata mutane da dama.
Kawo yanzu dai babu wata kungiya da ta dauki alhakin kaddamar da harin, sai dai wasu na danganta shi da kungiyar ABM mai sansani a lardin Sinai dake arewacin kasar ta Masar. (Saminu Alhassan)