in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'ar kasar Masar ta kaddamar da makon fina finan kasar Sin
2016-10-31 13:16:54 cri
Jami'ar Suez Canal ta kasar Masar da hadin gwiwar gidan radion kasar Sin CRI, sun bude makon nuna fina finan kasar Sin, bikin da aka yiwa lakabi da "hangen kasar Sin a zamanin yau".

Fim na farko da aka nuna a jami'ar ta Suez Canal, dake lardin Ismailia as arewa maso gabashin kasar ta Masar shi ne wani fim mai lakabin "Go Lala Go!, wanda aka juya zuwa harshen larabci, ya kuma samu lambar yabo ta kayatarwa.

Rahotanni sun bayyana cewa fim din ya samu karbuwa matuka musamman tsakanin daliban dake koyon Sinanci a cibiyar Confucius dake jami'ar su sama da 100.

Da take karin haske game da hakan, darakta mai lura da sashen gabas ta tsakiya a gidan radion CRI Zhang Li, ta ce gidajen talabijin da dama a kasar ta Masar, sun nuna matukar sha'awa ga fina-finan da sashen Larabci na gidan radion CRI ya juya zuwa Larabci.

Ta ce da dama daga wadanda suka kalli irin wadannan fina finai, na bayyana cewa suna ji a ransu, Masar da Sin na da al'adu da dama iri daya.

Ta ce fatan sashen ta shi ne Misirawa su kara fahimtar yanayin da yara mata ke ciki a kasar Sin, tare da kuma bura jan hankalin daliban kasar ta Masar zuwa ga sha'awar koyon Sinanci.

Baya ga fina finai, an kuma baje kolin rubuce rubuce game da shahararren marubucin wakoki da labaran nan dan kasar Sin wato Guo Moruo, ciki hadda tarihin rayuwar sa da aka wallafa da harsunan Sinanci, da turanci, da kuma larabci.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China