A yayin ganawarsu, Wang Yi ya bayyana cewa, a watan Afrilun bana, shugabannin kasashen biyu sun kuduri aniyar kafa dangantakar abokantaka ta samar da sabbin kayayyaki bisa manyan tsare tsare tsakaninsu. Wannan ne karo na farko da Sin ta kafa dangantakar abokantaka da sauran kasashen duniya mai alamar samar da sabbin kayayyaki. Hakan ba ma kawai zai sa kaimi ga bunkasa dangantaka tsakanin Sin da Switzerland zuwa wani sabon mataki ba ne, har ma zai zama abin koyi ga sauran kasashen duniya. A nan gaba, Sin za ta karfafa mu'amala tsakanin manyan jami'an kasashen biyu, da zurfafa hadin gwiwa a dukkan fannoni.
A nasa bangaren, shugaba Johann Schneider-Ammannya bayyana cewa, kasar Switzerland ta dora muhimmanci sosai kan kasar Sin, kuma za ta ci gajiyar bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin. Ana fatan bangarorin biyu za su tabbatar da dangantakar abokantaka irinta samar da sabbin kayayyaki bisa manyan tsare tsare tsakaninsu, domin samun karin sakamako a fannonin kiyaye tsarin cinikayya cikin 'yanci, da sa kaimi ga karfafa hadin gwiwa a fannonin tattalin arziki da cinikayya, da hada hadar kudi, da makamashi, da yawon shakatawa, da al'adu da dai sauransu.(Fatima)