in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wang Yi ya gana da babbar direktar hukumar WHO
2016-12-12 13:38:55 cri
A jiya Lahadi ne ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya gana da babbar direktar hukumar kiwon lafiya ta duniya wato WHO Margaret Chan a birnin Geneva na kasar Switzerland.

Mr. Wang Yi ya taya jami'ar murnar cimma nasarar gudanar da taron sa kaimi ga kiwon lafiya na duniya karo na 9 da ya gudana a birnin Shanghai na nan kasar Sin, yana mai cewa yanzu haka an kai ga daga matsayin kiwon lafiya a ajendar kasa da kasa. Ya ce gwamnatin kasar Sin ta dora muhimmanci sosai kan sha'anin kiwon lafiya a duniya, tana kuma nuna goyon baya ga ayyukan hukumar WHO. Kaza lika Sin za ta ci gaba da hada kai da hukumar WHO wajen tinkarar kalubalen kiwon lafiya a duniya gaba daya.

A nata bangare Margaret Chan ta yiwa gwamnatin kasar Sin godiya, game da goyon baya ga taron da ya gudana cikin nasara. Ta ce wannan muhimmin mataki ne a ajendar samun bunkasuwa mai dorewa a fannin kiwon lafiya nan da shekarar 2030. Kaza lika a cewar ta, Sin ta samar da gudummawa mai yawa a bangaren yaki da talauci, da kiwon lafiya a duniya. Ta kuma yi imanin cewa Sin za ta ci gaba da samar da gudummawa kan sha'anin kiwon lafiya na duniya, da samun bunkasuwa mai dorewa.

Har ila yau hukumar WHO na fatan za a kara gudanar da hadin gwiwa tare da kasar Sin a fannin kiwon lafiya bisa tsarin "ziri daya da hanya daya". (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China