in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wang Yi: Sin na kokari taimakawa kasashen Afrika wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali
2016-08-12 10:59:22 cri

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, dake ziyarar aiki a Kampala, ya bayyana a ranar Alhamis cewa taimakon kasar Sin ga aikin zaman lafiya da kwanciyar hankali a Afrika a tsawon shekarun baya baya nan ya janyo mata godiya da aminci daga wajen kasashen Afrika.

A yayin wani taron manema labarai na hadin gwiwa tare da takwaransa na kasar Uganda Sam Kutesa, mista Wang ya furta cewa kasar Sin na aiki a yanzu haka wajen tabbatar da alkawuran da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya dauka a shekarar da ta gabata, game da bayar da wani taimakon kudi na dalar Amurka miliyan 100 ga kungiyar tarayyar Afrika (AU) domin tallafawa kafa wata rundunar Afrika ta dindindin.

Mista Wang ya jaddada cewa Sin ta rike a zuciyarta tun yau da shekaru da dama game da ba da taimako wajen tabbatar da zaman lafiya, da gudanar da ayyukan shiga tsakani, da kuma kawo karshen yake yake a nahiyar Afirka.

Mista Wang ya kara da cewa, yanzu kasar Sin ta tura dakarun wanzar da zaman lafiya fiye da 2400 a cikin tawagogin wanzar da zaman lafiya guda bakwai na MDD a Afrika, musammun ma a Mali da Sudan ta Kudu, inda sojojin kasar Sin suke sadaukar da rayukansu a lokacin da suke gudanar aikinsu a farkon wannan shekara.

A nasa bangare, mista Kutesa ya nuna cewa Sin tana kasacewa daya daga cikin abokan hulda mafi tasiri da gaskiya a Afrika, ba kamar yadda kasashen yamma su kan yi ba, kasar Sin tana tsayawa kan taimakawa nahiyar wajen neman hanyoyinta na warware matsalolin dake adabar kasashen Afrika. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China