in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wang Yi: Kada MDD ta manta da farkon burinta wajen kare ka'idodin kundin mulkinta
2016-11-29 11:39:14 cri
A jiya Litinin, Mr. Wang Yi, ministan harkokin wajen kasar Sin da Mr. Antonio Guterres, mai jiran gadon babban sakataren MDD sun gana da manema labaru bayan sun yi shawarwari.

A yayin taron manema labaru, Mr. Wang Yi ya bayyana cewa, da farko dai, ya kamata MDD ta taka karin rawarta wajen tabbatar da zaman lafiya da neman bunkasuwar duk duniya, da kuma daukar kwararrun matakai wajen yada adalci da daidaito, tare da kuma yin karin yakini wajen neman yin hadin gwiwa da samun nasara tare tsakanin kasa da kasa.

Mr. Wang Yi ya kuma jaddada cewa, game da yadda MDD za ta iya taka rawarta kamar yadda ya kamata, shugaba Xi Jinping na kasar Sin yana da wani kalami, wato "kada a manta da farkon burinsa, kuma a yi kokarin neman ci gaba". Game da MDD, farkon burinta shi ne jerin ka'idojin da kasashe mambobinta suka kafa a lokacin da aka kafa ta. Yanzu, akwai rikice-rikice da dama da suke kasancewa a sassa daban daban na duniya, asalin dalilin da ya sa suka auku shi ne ba a bi ka'idojin MDD ba, har ma a kan karya wadannan ka'idoji. Sabo da haka, kasar Sin tana son hada kan sauran kasashen duniya wajen nuna goyon baya ga MDD, ta yadda za a iya tabbatar da ganin MDD ba za ta manta da farkon burinta wajen neman karin ci gaba, kuma za ta iya bayar da gudummawarta wajen tabbatar da zaman lafiya da bunkasuwar bil Adama ta hanyar yin gyare-gyare da kirkiro –kirkiro da sabbin hanyoyin gudanar da aikinta. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China