in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wang Yi ya gana da shugaban kwamitin IOC
2016-12-12 14:47:34 cri
A jiya Lahadi ne ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya gana da shugaban kwamitin wasannin Olympics na duniya wato IOC Thomas Bach, a birnin Lausanne dake kasar Switzerland.

Yayin ganawar ta su, Wang Yi ya bayyana cewa, kwamitin IOC muhimmiyar hukuma ce ta wasanni ta kasa da kasa, wanda ta samar da gudummawa wajen farfado da wasanni, da kara fahimtar juna a tsakanin jama'ar kasashen duniya. Kaza lika a cewar sa Sin na matukar goyon baya da halartar wasannin Olympics, ta kuma dauki bakuncin gudanar da wasannin Olympics a birnin Beijing, da gasar wasannin Olympics ta matasa ta birnin Nanjing cikin nasara. Yanzu haka kuma tana kokarin shirya gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi ta shekarar 2022 ta Beijing.

A nasa bangare, Bach ya bayyana cewa, Sin ta samar da muhimmiyar gudummawa ga sha'anin wasannin Olympics na duniya ta hanyoyi daban daban. Ya ce kwamitin IOC ya nuna yabo ga hadin gwiwar dake tsakaninsa da kasar Sin. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China