in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaminstan kasar Indiya ya gana da Wang Yi
2016-08-14 13:33:29 cri
A jiya Asabar firaministan kasar Indiya Narendra Modi ya gana da ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi a fadar firaministan kasar Indiya dake birnin New Delhi.

Modi ya bayyana cewa, yana dora muhimmanci sosai ga zumunta dake tsakaninsa da shugabannin kasar Sin, yana fatan za a yi musayar ra'ayoyi tare da shugabannin kasar Sin wajen kara bunkasa dangantakar dake tsakanin Indiya da Sin ta hanyar halartar taruka kamar taron koli na G20 na birnin Hangzhou, da ganawa tsakanin shugabannin kasashen kungiyar BRICS, da tarukan hadin gwiwar kasashen gabashin Asiya da dai sauransu. Ya ce kamata ya yi kasashen biyu su kara yin mu'amala da nuna goyon baya ga juna don gudanar da taron koli na G20 na birnin Hangzhou, taron shugabannin kasashen kungiyar BRICS yadda ya kamata. Kasar Indiya ta dora muhimmanci sosai kan dangantakar dake tsakaninta da kasar Sin, kana ba za'a canja manufar raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu bisa manyan tsare-tsare ba. Ya ce yin hadin gwiwa a tsakanin Indiya da Sin zai kawo alfanu ga kasashe masu tasowa.

A nasa bangare, Wang Yi ya bayyana cewa, kasashen biyu kasashe ne dake makwabtaka da juna, kana su ne kasashe masu tasowa, wadanda suke daukar nauyin tabbatar da zaman lafiya da samun bunkasuwa a duniya, da inganta karfin kasashe masu tasowa, da sa kaimi ga samun cigaba a kasashe daban daban na duniya. Sin tana maraba da kasar Indiya da ta samu cigaba, da nuna goyon baya ga kasar Indiya wajen taka muhimmiyar rawa kan harkokin kasa da kasa da yankuna, wannan matsayi ba zai canja ba, duk kuwa da irin canjin da ake samu a duniya. Raya dangantakar abokantaka ya dace da moriyar jama'ar kasashen biyu, da yanayin sabbin hanyoyin kasuwanci na kasa da kasa. Kasar Sin tana son yin kokari tare da kasar Indiya wajen inganta hadin gwiwar samun moriyar juna a tsakanin kasashen biyu. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China