Walid ya bayyana hakan ne a yayin wata ganawa tsakaninsa da manzon musamman na kasar Sin kan batun Syria Xie Xiaoyan a jiya Alhamis.
A ran 7 ga wata, Mista Xiaoyan ya isa babban birnin kasar Syria, Damascus, inda ya yi ganawa da Walid Muallem da kuma ministan kula da harkokin samar da sulhu tsakanin al'ummomin kasar Syria, Ali Haidar da wasu jami'an gwamnatin kasar da kuma wasu 'yan adawa na kasar ta Syria.
Haka kuma, a yayin taron maneman labarai da aka yi a birnin Damascus, Mr. Xie ya bayyana cewa, idan aka yi tsokaci kan batun Syria, a kan yaba wa kasar Sin kan matsayinta mai adalci da ta nuna kan wannan batu, ko da a halin yanzu, an dakatar da shawarwarin neman sulhu kan batun Syria, amma kasar Sin ba ta dakatar da kokarin da take yi ba ko kadan wajen farfado da shawarwari a kasar ta yadda za a warware matsalar kasar ta hanyar siyasa.
A ran 5 ga watan nan da muke ciki, an kada kuri'u kan daftarin kudurin dake shafar yanayin birnin Aleppo na kasar Syria a taron kwamitin sulhu na MDD, inda kasar Sin, da Rasha da kuma kasar Venezuela suka kada kuri'un nuna rashin amincewa, sakamakon haka, ba a kai ga zartas da daftarin ba.
A ganin kasar Sin, wasu kasashe sun kare aniyarsu ta kada kuri'a a kan kudurin ba tare da tattaunawa sosai kansa ba, lamarin da ya sa, akwai sabani mai tsanani a tsakanin bangarorin daban daban da abin ya shafa dangane da wannan batu, kuma ba zai taimaka ga warware matsalar ta Syria ba. (Maryam)