Cikin kudurin hukumar haramta makamai masu guba da aka zartas a ranar 11 ga wata, an zargi sojojin gwamnatin Syria, da kuma kungiyar masu tsattsauran ra'ayi ta IS da yin amfani da makamai masu guba a kasar Syria, kudurin ya kuma nuna goyon baya ga gudanar da bincike a kan na'urorin soja, da kuma hukumomin nazari a cikin kasar Syria.
Game da hakan, ma'aikatar harkokin waje ta Syria ta nuna rashin yarda da wannan zargi, kuma a cewarta, ana nuna mata bambanci ne kawai.
Sanarwar ta ce, wasu kasashe sun mai da hukumar haramta makamai masu guba a matsayin abin da zai taimaka musu cimma burinsu na siyasa. Yanzu haka dai gwamnatin Syria tana tantance kudurin, kuma nan ba da jimawa ba, za ta fitar da takarda a hukunce don bayyana matsayinta.(Lubabatu)