Sanarwar ta ce, farmakin sun kuma lalata asibitoci a gabashin birnin Aleppo, dake arewacin kasar ta Syria, har ma dukkansu ba su iya aiki. Ban da wannan kuma, sanarwar ta yi Allah-wadai da farmakin da aka kaiwa makarantu, wadanda suka haddasa rasuwar dalibai.
Baya ga haka, Ban ya gargadi bangarori daban daban da rikicin ya shafa cewa, kai farmaki kan fararen hula da na'urorinsu da gangan tamkar laifin yaki ne, saboda haka ya yi kira ga bangarori daban daban da su dakatar da wadannan hare-hare. Ban ya bayyana cewa, duk wadanda suka tayar da farmakin za su amsa laifinsu. Bayan haka kuma, Ban ya yi kira ga bangarori daban daban da su tabbatar da 'yancin tafiye-tafiye na fararen hula, tare kuma da ba da tabbacin ganin an samar da taimakon jin kai ga mutanen da suke bukata ba tare da matsala ba.
A kwanankin baya ne, al'amura suka kara tsananta a wasu sassan kasar Syria, inda aka rika kaiwa wasu makarantu da asibitocin da ke karashin ikon gwamnatin Aleppo da dakaru masu adawa da gwamnati farmaki.(Bilkisu)