Zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Liu Jieyi, ya bayyana cewa, bisa yanayin da ake ciki a yanzu, kamata ya yi kasashen duniya su tsaya kan warware batun Syria a siyasanci, kana da yin kokari tare don warware batun ta hanyar yin shawarwari da nufin lalibo hanyar kawo karshen rikicin tun da wuri.
Wannan shirin kudurin ya samu kuri'un amincewa 11, kuri'un adawa 3, tare kuma da kuri'ar janye jiki guda 1, inda kasashen Rasha, Sin da Venezuela suka nuna adawa, kasar Angola ta janye jiki. Kudurin ya bukaci a tsagaita bude wuta na tsawon kwanaki 7 a Aleppo.
Liu Jieyi ya ba da jawabi bayan jefa kuri'ar, inda ya bayyana cewa, kamata ya yi matakan da kwamitin sulhun ya dauka za su amfana wa ayyukan sake farfado da tsagaita bude wuta, da shawarwarin zaman lafiya ta hanyar siyasa, da yaki da ta'addanci na hadin gwiwa, da kuma ba da taimakon jin kai.
Liu ya kara da cewa, a cikin kudurin an gabatar da hakikanan matakai wajen sassauta halin jin kai a Syria, kasashe mambobin kwamitin sulhu, ciki har da kasashe masu gabatar da shirin sun yi iyakacin kokari don neman ra'ayi bai daya a kai. Idan aka ci gaba da irin kokarin, kasashe mambobin za su iya nuna ra'ayi bai daya ga waje, hakan za a iya hana a mai da batun jin kai a matsayin wani batun siyasa. Amma, idan ana daukar matakai kan wannan shirin kuduri kafin a kawar da bambanci sosai dake kasancewar a tsakanin bangarori daban daban, wannan ba shi da amfani wajen kokarin diplomasiyya da wasu kasashe suka yi, kuma ba zai kyautata halin da kasar ta Syria ke ciki ba. (Bilkisu)