Haka kuma, shugaba Assad ya ce, tun da farko gwamnatin kasar Syria ta tsai da kudurin 'yantar da yankin Aleppo, sabo da birnin ya kasance muhimmin birni kamar babban birnin kasar Damascus yake a duk fadin kasar ta fannin siyasa da tattalin arziki.
Bugu da kari, rundunar sojan kasar ta bayyana a ran 7 ga wata cewa, sojojin gwamnatin kasar sun kwace tsohon yankin birnin Aleppo gaba daya sakamakon matakan sojan da suka dauka a wannan rana.
Dangane da wannan lamari, kungiyar sa ido kan yanayin hakkin dan Adam wadda hedkwatarta dake birnin London na kasar Burtaniya ta bayyana cewa, dakarun kungiyar adawa da gwamnati sun fara janye jikinsu daga tsohon yankin birnin Aleppo zuwa kudancin birnin, hakan ya sa, gwamnatin kasar Syria ta kwace kashi 8 bisa 10 na yankin dake hannun dakarun adawa a birnin Aleppo. (Maryam)