A cewar jami'in kasar Sin, yanzu haka yanayin da ake ciki a kasar Syria yana da sarkakiya matuka. Saboda haka, kamata ya yi, kwamitin sulhu na MDD ya yi kokarin ganin bangarori daban daban sun cimma ra'ayi daya, tare da kiyaye hadin kan mambobin kwamitin, ta yadda za a samu damar taimakawa kokarin warware maganar Syria ta hanyar lumana. A sabili da haka, kasar Sin ta ki yarda da yadda aka nemi zartas da wani shirin da ake da sabanin ra'ayi a kansa. Dabarar da wasu kasashen suka bullo da ita ta tilastawa mambobin kwamitin sulhu zartas da wani kuduri ba za ta taba yin amfani ba, sai dai ta jawo baraka ga kwamitin, in ji jami'in kasar Sin.(Bello Wang)