in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Cote d'Ivoire na son koyi da salon kasar Sin domin samun cigabanta
2016-08-11 10:57:05 cri

Kasar Cote d'Ivoire tana son yin koyi da kasar Sin domin neman cigabanta, in ji wasu jami'an kasar a birnin Man dake yammacin kasar a ranar Laraba.

Ministan harkokin wajen kasar Cote d'Ivoire, Albert Toikeuse Mabri, dake magana a yayin wata ziyarar jakadan kasar Sin dake Cote d'Ivoire Tang Weibin a yankin, ya bayyana cewa Sin a yanzu tana cikin jerin kasashen duniya dake a sahun gaba dalilin jajircewa wajen aiki.

Wannan misali na aiki da jajircewa ya kamata suke kasance darasi a yankin Tonkpi dake kunshe da dimbin albarkatu, in ji mista Mabri.

A cewar shugaban kwamitin yankin Tonkpi, Gaston–Aime Woi Mela, kasar Sin da ta tashi ba kowa amma yanzu ta yi wani tashin gwabron zabo na mamaki domin shiga, kuma wannan a cewarsa, wani misali ne mai ban al'ajabi.

Muna bisa hanya guda tare da shugaban kasar Cote d'Ivoire Alassane Ouattara da ya nuna cewa kasarsa na son yin koyi da salon kasar Sin domin kasancewa wata kasa mai tasowa a kewayen shekarar 2020, in ji mista Woi Mela. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China