in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Cote d'Ivoire ta yi maraba da hadin gwiwar da ke tsakanin ta da Burkina faso a yaki da ta'addanci
2016-07-29 18:54:17 cri
Firaministan kasar Cote d'Ivoire Daniel Kablan Duncan ya yi maraba da hadin gwiwar da ke tsakanin kasarsa da kasar Burkina Faso kan yaki da ta'addanci.

Duncan wanda ya bayyana hakan lokacin da ya ke jawabi a bude taron hadin gwiwa na taron kolin yarjejeniyar hadin gwiwar abokantaka karo na biyar tsakanin kasashen Cote d'Ivoire da Burkina Faso, ya ce yana maraba da kyakkyawan misali na hadin gwiwar da hukumomin tsaron kasashen biyu suka nuna,bayan hare-haren da aka kai a Ouagadougou da Grand Bassam.

Idan ba a manta ba a ranar 13 ga watan Maris na wannan shekara ne aka kai wani harin ta'addanci a wurin shakatawa na Grand Bassam na Cote d'Ivoire, harin da ya haddasa mutuwar mutane 19, kana bayan wasu 'yan watanni aka sake kaddamar da wani mummunan harin ta'addanci a Ouagadougou,babban birnin kasar ta Burkina Faso, inda mutane 30 suka mutu.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China