in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen Nijar da Libiya na tattaunawa kan dangantakar tsaronsu
2016-09-08 10:55:46 cri

Rikicin Libiya da sauran batutuwan tsaro a bangaren kan iyakar Nijar da Libiya sun kakace jerin ganawa a ranar Talata da yamma a birnin Yamai tsakanin hukumomin Nijar da wata babbar tawagar Libiya dake karkashin jagorancin shugaban majalisar wakilai, Aguila Saleh, da kuma faraministan kasar, Abdallah Assani.

A yayin wani zaman taro, an mai da hankali game da wajabcin tabbatar da kwanciyar hankali a Libiya, a matsayin wani ginshikin zaman lafiya mai karko a wannan shiyya.

Sau da dama ne, hukumomin Nijar suka rika zargin Libiya da zama a halin yanzu wata cibiyar janyo fitina da zaman dar dar ga kasashen dake yankin Sahel, dalilin kasancewa yawan sojojin sa kai masu makamai a yankin kudancinta tun lokacin da kasashen yammacin duniya suka kori gwamnatin Mouammar Kadhafi, tare da kashe shi a shekarar 2012.

Haka kuma, shugaban kasar Nijar Mahamadou Issoufou ya rika kira kullum da a tura sojojin kasa da kasa a Libiya domin murkushe sojojin sa kai domin mai do da zaman lafiya a wannan kasa.

A cikin watan Janairun shekarar 2015, a yayin wata hira da gidan rediyon RFI, shugaban Nijar ya yi watsi da batun duk wata tattaunawa tare da kungiyoyi masu makamai. Kuma wannan haka yake game da kasar Libiya, in ji shugaba Issoufou.

Kafin komawarsu gida, tawagar Libiya din ta samu ganawa tare da shugaba Issoufou. Kasar Nijar dai na raba kan iyaka guda tare da Libiya bisa tsawon kilomita 400. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China