Mataimakin firaministan gwamnatin kasar Moussa al-Koni, ya bayyana cewa, an riga an kai dukkan makamai masu guba na kasar zuwa kasashen waje don lalata su.
Majalisar dokokin kasar Denmark ta jefa kuri'a a ranar 19 ga wannan watan nan, inda aka amince da gwamnatin kasar ta tura jiragen ruwa don halartar aikin jigilar makamai masu guba, daga kasar Libya zuwa kasashen waje. Game da hakan ministan harkokin wajen kasar Denmark Kristian Jensen, ya bayyana cewa an gudanar da jigilar makaman zangon karshe ne, don hana fadawar su hannun kungiyoyi masu tsattsauran ra'ayi. (Zainab)