Hakan dai na kunshe ne cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar, wadda kuma ke cewa 'yan tawayen dake cikin yankin, na da damar fita ta titin Castello dake arewacin Aleppo, da kuma hanyar Souk al-Khair mai iyaka da arewa maso yammacin lardin Idlib.
Kaza lika sanarwar ta umarci fararen hula da su fice daga yankin ta wasu hanyoyi 6, zuwa yankunan dake karkashin ikon gwamnatin kasar a yammacin Aleppo.
Ba wannan ne dai karon farko da aka fidda irin wannan sanarwa ba, domin kuwa ko da cikin watan da ya gabata, sai da mahukuntan Rasha da na Syria suka bayyana irin wannan tanaji na kwanaki 3, sai dai kuma hakan bai yi amfani ba. A wancan lokaci tsagin gwamnatin kasar ya zargi 'yan adawa da hana fararen hula fita daga gabashin yankin na Aleppo.
A jiya laraba wasu rahotanni sun bayyana yadda mayakan 'yan tawayen dake tunga a gabashin Aleppo suka hallaka gwamnan fararen hula dake da nufin fita daga yankin.
An ce wani sashe na 'yan adawar na cazar mutane makudan kudade, kafin su basu damar fita daga wannan yanki. Hakan na kuma faruwa ne yayin da fada ke ci gaba da kazanta tsakanin sojin gwamnati da na 'yan adawar a yammacin Aleppo.