Koda yake, wannan ba shine karon farko da Amurkar ta kaddamar da hare hare kan mayakan IS a Libya ba, sai dai wannan shine karon farko da gwamnatin hadakar Libyan ta bukaci Amurkar ta kaddamar da hare haren ta jiragen sama a hukumance. A cewar mai Magana da yawun ma'aikatar tsaro ta Pentagon Peter Cook, Amurkar ta kaddamar da hare haren ne a Sirte, wani birnin dake yankin tekun Mediteraniya, bayan da shugaba Barack Obama ya bada umarni.